Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin Najeriya 36 sun rubuta wa Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed Wasi?a, inda su ka garga?e ta cewa kada fa ta sake ta biya dala miliyan 418 ga yan kwangilar da gwamnonin su ka ce ‘yan wanki ne.
Wasi?ar dai sun rubuta ta ne ta hannun lauyan su Femi Falana, wanda ya rubuta mata hatsarin da ke tattare da biyan ku?a?en.
Falana ya nemi a madadin gwamnonin cewa Minista Zainab ta janye umarnin da ta ba Ofishin Kula da Basussuka (DMO) cewa ya fara shirin bayar da takardun al?awarin biyan ku?a?en a cikin wasu ?ayyadaddun lokuta ga yan kwangilar.
Gwamnonin sun ce ya kamata Minista Zainab ta fahimci cewa sun shigar da ?ara a Kotun ?oli, kuma Kotun ?oli ba ta ce a biya ku?a?en ba, domin har?alla ce da dungu da wanki kawai.
Ku?a?en wa?anda dala miliyan 418 ne, idan aka canja su zuwa dala a farashin gwamnati na dala 1 Naira 410, za su kama naira biliyan 171 kenan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya wani bashin da aka yi i?irarin ana bin jihohi 36 da ?ananan hukumomi 774.
Adadin bashin ya kai dala miliyan 418, kwatankwacin naira biliyan 159 da ya amince a biya wasu mutum shida, duk kuwa da cewa Gwamnonin Najeriya sun da?e su na nuna wa Buhari cewa babu tabbaci ko wata ?wa??warar shaida ko hujjar an yi ayyukan a jihohi har na wa?annan adadin ma?udan ku?a?e.

