Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnoni Ne Matsalar Najeriya – Bello Muktar

Honorabul Bello Muktar ?an siyasa kuma mai sharhi akan al’umuran yau da kullum ya bayyana gwamnonin kasar nan a matsayin ummul aba’isin rashin aiwatar da wasu muhimman abubuwan da zai kawo wa kasar nan cigaba a fannoni daban – daban. Rashin sanin hakan yasa wasu da dama ke ganin wallen gwamnatin tarayya a lokuta da dama.

Bello Muktar ya bayyana cewa ?arfin ikon da kundin tsarin mulkin kasar nan yaba gwamnoni yayi yawa kuma hakan na daya daga cikin dalilan da yasa har yanzu talakan ?asar nan bai anfana da romom mulkin dimokaradiyya.

Bello ya bayyana hakan ne a shirin Dialogue da ake gabatarwa a gidan talbijin na liberty TV dake kaduna.

“Gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ba ?ananan hukumomin ‘yancin cin gashin kansu wanda sune ke kusa da talakan kasar nan amman Gwamnoni suka yi watsi da shirin saboda son zuciyar su.
Gwamnatin tarayya ta ?ullo da shirin Ruga na makiyaya domin kawo karshen rigingimun manoma da makiyaya wanda ke janyo asarar rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya shekara da shekaru amma a kasar nan wasu gwamnonin suka ce hakan bazai taba faruwa ba.

Gwamnatin Tarayya ta ?ullo da shirin Almajiri domin ba yaran mu marasa galihu ilimi a kasar nan da kau dasu a titunan kasar nan, shima haka wasu gwamnonin suka yi watsi da shirin.

Idan muka dawo kan matsalar tsaro kowane gwamna zai gaya maka bai da ikon ba jami’an tsaro umurni a jihar sa duk da karfin ikon da Gwamna yake dashi a siyasance.
Wanda hakan kuma wani tsari ne daban da kundin tsarin mulki yaba kowa iyakar sa.

Akwai matakan da gwamnati ya kamata tabi na anfani da kimiyya da kuma gayyatar manyan kasashen duniya domin suzo su aiwatar da wani shiri nasu na musamman akan makamashin Nukiliya ko kuma sarrafa wasu ma’adanan da muke dasu a kasar nan, wadannan kasashen da zamu gayyata sune zasu kafa shi a kasar kuma su dinga sarrafa shi karkashin wata kayadadden yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Idan aka basu ikon kula da wannan aikin babu yadda zasu bar wasu yan ta’adda su zauna su ci karensu babu babbaka a dazukan kasar nan kamar yadda muke gani a halin yanzu.
“A daji kamar na sambisa ko kuma wani babban daji a kasar nan ne za a kakkafa wannan kayayyakin aikin da manyan kasashen duniya zasu zo dashi”.

Da wannann hikimar ka?ai inda gwamnatin Najeriya zata ba kasa kamar Rasha wannan aikin za kaga ankawo karshen ‘yan bindiga da duk sauran ‘yan ta’addan da ke ?uya a dazukan kasar nan.

Exit mobile version