Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin mallakar sama da kadada dubu 720,000 daga jihohi daban-daban don inganta amfanin gona,
Ministan Noma da Raya Karkara, Alh. Sabo Nanono ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a wata ganawa da ya yi da shugabannin gudanarwa na maaikatu da kuma manyan jamian gudanarwa na Maaikatar aikin Gona ta tarayya da raya Karkara a Abuja.
Ya ce maaikatarsa ??ta tanadin fili tsakanin kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha da nufin bunkasa bangaren noman kasar nan. Gwamnatin Tarayya za ta mallaki kadada dubu 720,000 daga dukkan jihohin 36.
Ministan ya kara da cewa A yanzu haka, maaikatar ta dauki kwararan matakai na sanya tsarin binciken aikin gona, da samar da kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha don amfanin aikin gona, da kuma inganta ayyukan gona da hadin kai a duk ?asar.
Tsammani mu shine tura ingantattun iri, fadada yankin noma da tallafawa ayyukan noma a kasar..

