Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Nasarar Gano Masu Daukar Nauyin Boko Haram

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke sa ido da tattara bayanan sirri kan hada-hadar ku?i a Najeriya ta gano masu ?aukar nauyin ta’addancin Boko Haram 96 da kuma 424 da ke taimaka musu.

Ministan watsa labarai da al’adu Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai kan ya?i da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take yi.

Ministan ya ce hukumar ta gano kamfanoni 123 da kuma masu sana’ar canjin ku?i 33 da ke da ala?a da ta’addancin na kungiyar.

Sai dai Lai Mohammed ?in bai bayar da bayanai ba kan sunayen mutanen da kamfanonin da ke da ala?a da ta’addanci.

Exit mobile version