Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Dage Lokacin Hada Layin Waya Da Lambar Dan Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sake kara wa’adin ha?a layin waya (SIM) da lamabar katin ?an kasa (NIN) har zuwa 31 ga watan Oktoba, karo na shida tun watan Disamban shekarar da ta gabata.

A wani jawabin ha?in guiwa da hukumar sadarwa ta ?asa (NCC) ta fitar a shafinta na Facebook, ranar Lahadi, ya nuna cewa an ?auki wannan matakin ne biyo bayan ro?on masu ruwa da tsaki domin shirin yakai har kananan yankuna, yan ?asashen waje da kuma yan Najeriya dake ?asashen duniya.

Jawabin wanda ke ?auke da sanya hannun kakakin NCC, Ikechukwu Adinde, da takwaransa na NIMC, Kayode Adegoke, ya nuna cewa karin wa’adin zai magance karancin rijista a makarantu da asibitoci, kamar yadda kididdiga ta bayyana.

Wani sashin jawabin yace: “An ?auki matakin ne biyo bayan nazari kan cigaban da ake samu kan shirin na ha?a SIM-NIN a fa?in ?asar nan.” “Zuwa ranar Asabar 24 ga watan Yuli, akwai na’urorin yin rijista 5,500 a ciki da wajen ?asar nan domin saukaka wa mutane wajen rijistar NIN da kuma ha?a lambar da SIM.”

Shugaba Buhari ya amince da karin Jawabin ya ?ara da cewa gwamnatin shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ta amince da karin wa’adin a kokarinta na saukakawa yan Najeriya dake ciki da wajen ?asa. Hakanan kuma domin saukaka wa mazauna ?asar a bisa doka su mallaki lambar NIN ta hanyar amfani da damar karin wa’adin.

Kusan mutun miliyan 60 sun mallaki NIN Jawabin yace: “Zuwa yanzun yan Najeriya kimanin miliyan 59.8m sun yi rijistar NIN, tare da ha?a layukan waya 3-4 kowace lamabar.” “Bisa adadi mai yawa na cibiyoyin rijista a ciki da wajen ?asa da kuma wasu da za’a ?ara nan gaba, kowane ?an Najeriya da wanda doka ta basu damar zama zasu samu damar mallakar NIN.”

Exit mobile version