Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Roki Gwamnoni Su Tabbatar Shinkafar Da Aka Basu Ta Kai Ga Talakawa

IMG 20240708 WA0041

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi kira ga gwamnonin Jihohi su tabbatar shinkafar da aka basu takai ga hannun talakawa.

Mnistan ya?a labarai Alhaji Mohammed Idris ne ya yi wannan kiran a Abuja, lokacin da yake karin haske dangane da matakan da gwamnatin Tinubu ke ?auka na magance matsalar yunwa dake addabar ‘yan ?asar.

A ranar Litinin ?in wannan mako ne gwamnatin tarayya ta sanar cewa ta bai wa gwamnoni tirelolin shinkafa wa?anda za su raba wa al’umma domin rage ra?a?in yunwa.

A lokacin da ya yi bayani bayan taron ?angarren zartaswa na gwamnatin tarayya, ministan ya?a labarai Mohammed Idris ya ce an bai wa kowace jiha ha?i da Abuja tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.

Ya ce kowace tirela tana ?auke da buhun shinkafa 1,200 kg25 da aka ba gwamnonin jihohi a wani mataki na rage wa talakawa ra?a?in ?arancin abinci da tsadarsa da ake fuskanta a ?asar.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabu?ata a matakin jiha da ?ananan hukumomi.

Hakan na nufin kowace jiha, da kuma babban birnin tarayya za ta samu jimillar buhunan shinkafa masu nauyin 25kg guda 24,000.

Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake ala?antawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.

Exit mobile version