Kamfanin samar da man Nijeriya na NNPC ya kori maaikatan sa 850 kuma akasarin su sun fito ne daga matatun man kasar da basa aiki yadda ya dace.
Sakataren kungiyar manyan maaikatan man kasar na PENGASSAN, Lumumba Okugbawa yace maaikatan da aka sallama sun kunshi kwararru da wadanda ba kwararru ba, tare da wadanda ke taimakawa wajen tafiyar da matatun man.
Kamfanin man NNPC bai yi bayani kan korar maaikatan ba, sai dai a makwannin da suka gabata, shugaban sa Mele Kyari ya bayyana damuwa kan asarar da kamfanin keyi wajen rashin ingantaccen aikin da matatun man kasar keyi, abinda ya sa Najeriya ta dogara da kasashen ketare domin samarwa alummar kasar tacaccen man fetur.
A watan Mayun da ya gabata, kamfanin NNPC yace yana da maaikata sama da 6,600 dake karbar albashi daga lalitar sa.
Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suka dogara da albarkatun man fetur domin samun kudaden shigar da take amfani da su.

