Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wasu bayanai da suka fito daga ma’aikatar albarkatun man fetur ta ?asa ta ce gwamnatin tarayya ta bayar da kusan nairan biliyan 173.2 domin daidaita farashin sama da lita biliyan 11.6 na man fetur tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022 a fa?in ?asar.
Gwamnatin Buhari ta biya ku?in daidaita farashin man ne ta hanyar hukumar da ke kula da hada-hadar kasuwancin man fetur ta ?asar.
Inda hukumar ?ayyade farashin man fetur ta NMDPRA ke tabbatar da daidata farashin man ta hanyar biyan ku?in dakon man a manyan motoci zuwa gidajen mai a fa?in ?asar.
To sai dai duk da wa?annan biliyoyin ku?a?e da hukumar ke cewa ta biya, domin daidai farashin, har yanzu ana sayar da man a mabambantan farashi a fadin ?asar.

