Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Sabunta ?arfin Lantarki – Ministan Lantarki

Ministan ?asa a Ma’aikatar lantarki Mista Goddy Jedy Agba, ya bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya amince da ?arin ?arfin hasken lantarki, domin bunkasar harkokin kasuwanci Makarantu da Asibitoci a fa?in ?asar.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ?addamar na’urorin lantarki masu nauyin kilowatt 100 masu amfani da hasken rana a yankin ?aramar Hukumar Kiwon da ke jihar Ebonyi.

Kamar yadda ya bayyana tsarin sabunta karfin lantarki shine mafita wajen cike gi?in da ake fama da shi da ?arancin lantarki a Najeriya.

Ministan ya bayyana wannan tsarin a matsayin wanda zai taimaka wajen ha?aka harkoki musanman a ?auyuka sashen noma da kasuwanci, kuma ba da jimawa nan ba jama’ar Najeriya zasu fara cin gajiyar wannan tsarin.

“Wannan yana daga cikin muhimman kudurori na shugaban kasa Buhari na ganin an yalwata kasar da hasken lantarki.

Ma’aikatar lantarki tana yin dukkanin mai yiyuwa kuma za ta cigaba da hakan wajen ganin ta ciyar da ?asar gaba ta fuskar domin cimma kyawawan manufofin Shugaban ?asa.

Exit mobile version