Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Raba Tallafin Korona A Arewa Maso Gabas

Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin kudi ga talakawa da gajiyayyun mata wadanda rikicin Boko Haram da annobar korona ya ritsa da su a Shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Ministar ma’aikatar jin ?ai da walwala ta Gwamnatin tarayya Hajiya Sadiya Farouk, a yayin ?addamar da shirin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, tace burin tallafin shine samar da wadataccen jari ga matan domin bun?asa tattalin arzikin ?asa.

Sadiya Faruq ta ?ara da cewa gwamnatin jihar Yobe ta amshi kudi fiye da Naira Miliyan 980 karkashin shirin gwamnatin tarayya na raba kudade tun daga fara shi.

Kimanin kananan hukumomi 6 ne ke cin gajiyar shirin a jihar ta Yobe, kuma shirin zai fa?a?a ya game dukkanin ?ananan hukumomin Jihar ya ketara sauran Jihohin dake Shiyyar gaba ?aya.

Minista Sadiya ta yi bayanin cewa za’a raba dubu 20 ga kimanin mutane dubu 10 domin rage ra?a?in annobar cutar korona. An kirkiro shirin tallafin kudin ne a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin rage ra?a?in talauci.

Exit mobile version