Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shafin Tiwita A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumunta na Twitter a Nijeriya kamar yadda gwamnatin ta sanar a shafin ma’aikatar Labarai da al’adu a Twitter.

Ministan sadarwa da al’adu, Lai Mohammed ne ya sanar da dakatarwa a ranar Juma’a a Abuja, yana mai cewa ana amfani da shafin wurin aikata abubuwa da ke barazana ga hadin kan Nigeria.

Ministan ya kuma ce gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai, NBC, ta fara aikin bada lasisi ga dukkan dandalin sada zumunta da ake amfani da su a kasar.

Gwamnatin tarayya ta fara sa-in-sa da Twitter bayan goge wani sashi na rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi inda ya gargadi mambobin haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, su daina lalata kayan kasa.

Da ya ke martani kan goge rubutun na Buhari a ranar Laraba, Ministan Labarai da al’adu ya ce bai san dalilin da yasa shafin na Twitter bai goge rubutun da shugaban IPOB Nnamdi Kanu da masu goyon bayansa ke yi ba na tada zaune tsaye.

“Twitter na da dokokinta; ba dokar duniya bane. Idan akwai abin da ya bata wa shugaban kasa rai a ko ina, yana da ikon bayyana ra’ayinsa. “Mu daina misalta abu biyu da ke da banbanci.

Idan an haramta kungiya, tana da banbanci da kungiyar da ba a haramta ba.” “Shugaban kasa na da ikon nuna bacin ransa game da duk wata kungiya da ke umurta mambobinta su kashe ‘yan sanda, su kai hari gidajen gyaran hali, su kashe gandirebobi, Me yasa ake nuna wariya?.

“Ban taba ganin idan a duniya kungiya musamman wadda aka haramta ke umurtar mambobinta su kaiwa gwamnati, yan sanda, da sojoji hari kuma a kyale ta ba. “Babu yadda za a yi ka halasta maganganu na umurnin a kashe yan sanda ko duk wani wanda ra’ayin ku bai zo daya ba.”

Exit mobile version