Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya amince da ?age aikin ?idayar a ?asar wanda aka tsara daga ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayu.
Yana cewa a bari gwamnati mai zuwa ta sanya lokacin da ya dace.
Amincewar shugaban da wannan mataki, ta zo ne bayan wata tattaunawa da ya yi da mambobin Majalisar Zartaswa ta Tarayya da shugaban Hukumar ?idaya ta ?asa Nasir Isa Kwarra da ma’aikatansa a Abuja jiya Juma’a.
Ya dai yaba wa ?o?arin hukumar kan shirinta na aiwatar da ?idaya mai tsafta, ta hanyar samar da na’u’rorin zamani da za a yi amfani da su domin aza tubalin ?idayar da za a dogara da ita a nan gaba.
Muhammadu Buhari ya kuma nusar da cewa an kammala aikin rarraba yankunan da za a ?idaya da gwajin ?idaya na farko da na biyu, tare da ?aukar ma’aikatan wucin gadi da horas da su. Sannan kuma an samo jami’an ayyukan dijital da na’urorin fasahar zamani ta intanet.
Mahalarta taron dai sun gamsu cewa akwai bu?atar gudanar da ?idayar idan aka yi la’akari da cewa rabon da Najeriya ta yi ?idaya, shekara 17 kenan, kuma abubuwa da yawa sun sauya, don haka za a bu?aci sake sanin adadin ‘yan Najeriya.
Sanin nasu a cewar zauren taron na fadar shugaban ?asa, zai taimaka wajen gina duk wani ci gaban ?asa da zai yi daidai da adadin ‘yan ?asar da nufin bun?asa rayuwarsu.
Shugaba Buhari ya umarci Hukumar ta ci gaba da shirye-shiryen da ta fara na ?idayar 2023, domin kada a watsar da ?o?arin da aka faro, ta yadda gwamnati mai zuwa za ta samu bayanan da suka kamata don sau?a?a mata cimma burin wannan shiri.
Cikin mahalarta taron, akwai ministan shari’a Abubakar Malami da ministar kudi da tsare-tsare Zainab Ahmed da ministan ya?a labarai Alhaji Lai Mohammed.
A watan jiya ma, sai da shugaban hukumar ?idayar jama’a ta Najeriya Nasir Isa Kwarra ya sanar da ?age aikin sakamakon jinkirta za?en gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a ?asar.
?age aikin ?idayar zai kasance wani babban koma-baya ga Najeriya, ?asa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka.
Sanarwar hukumomi ba ta yi ?arin haske a kan dalilan da suka janyo dakatar da aikin ?idayar, kwana hu?u kafin a fara shi ba.
An dai kashe ma?udan ku?a?e, kuma an shafe tsawon lokaci ana shirye-shirye don wannan gagarumin da aka ?age a yanzu.
Babu wani tabbaci a kan takamaiman lokacin gudanar da ?idayar jama’a ta gaba a Najeriya, duk da yake bisa ?a’ida kamata ya yi a yi aikin shekara bakwai da ta wuce.

