Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana wa manema labarai cewa Gwamnatin Tarayya ta biya dala miliyan 218, matsayin somin-ta?in fara aikin titin jirgin ?asa daga Kaduna zuwa Kano.
Amaechi ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce tantagaryar adadin ku?a?en kwangilar dala biliyan 1.2 ne. Amma daga cikin an fara biyan dala miliyan 218, domin a fara aikin titin cikin wannan wata na Yuli da mu ke ciki.
Amaechi ya ce yanzu hankalin gwamnatin tarayya ya karkato a kan aikin titin jirgin ?asa daga Kaduna zuwa Kano, tunda an rigaya an kammala na titin Legas zuwa Ibadan.
A yanzu abin da ya rage a biya kudin aikin su ne dala miliyan 900. Kuma nan da makonni ka?an masu zuwa za a sake biyan dala miliyan 100. Inji Amaechi wanda ya ce ya na sa ran zuwa ?arshen wannan shekara za a yi ?o?ari a biya dala miliyan 600.
Ya kuma yi magana kan sauran titinan da Gwamnatin Tarayya ta ?udidi aniyar shimfi?awa, kuma duk na jirgin ?asa daga na Maiduguri da na Ibadan zuwa Kano, da na Legas zuwa Calabar.
Ya ?ara da cewa an fara biyan ku?in somin-ta?in aikin titin jirgin ?asa na Kano daga Kaduna daga cikin kasafin gwamnatin tarayya.
Akwai kuma sauran kashin ku?a?en wanda China ce za ta biya, amma ba ta fara biyan ba tukunna.
Kada ku tambaye ni inda Najeriya ta samu ku?in da ta biya. Domin a matsayi na na Kirista, gidan Shai?an ne ka?ai ba zan iya zuwa neman bashi ba. Inji Minista Amaechi.

