Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sabon Tsarin Kawar Da Yunwa A ?asar

Gwamnatin Najeriya ta amince da wani shiri na shekara biyar da zai yi aikin rage yunwa a ?asar da kuma rage yawan yara da ba sa samun abinci mai gina jiki.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriya, Laolu Akande, shi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.

Cibiyar National Council on Nutrition ce ta sahale fara aiwatar da shirin, wadda Mataimakin Shugaban ?asa Farfesa Yemi Osinbajo ke shugabanta.

An yi wa shirin la?abi da “National Multi-Sectoral Plan of Action for Food and Nutrition (NMPFAN) 2021-2025” wato tsarin samar da abinci mai gina jiki na ?asa na shekarar 2021-2025.

Shirin zai taimaka wurin aiwatar da tsare-tsaren da?ile yunwa da kuma ?arancin abinci mai gina jiki a fa?in Najeriya.

“Shirin da aka amince da shi zai rage adadin mutanen da ke fama da ?arancin abinci mai gina jiki da kashi 50 cikin 100 sannan ya ?ara yawan shayar da yara nonon uwa zuwa kashi 65 cikin 100,” a cewar sanarwar.

Kazalika, zai rage yawan yara ‘yan ?asa da shekara biyar da ba sa girma yadda ya kamata zuwa kashi 18 cikin 100 nan da 2025.

Exit mobile version