Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara ta yi i?irarin gwamnatin Muhammad Bello Matawalle ta bar wa sabuwar gwamnatin PDP, ?ar?ashin gwamna Dauda Lawal Dare kimanin naira biliyan 20.5 da kuma dala miliyan 1.9 a lalitar gwamnati.
APC cikin wata sanarwa da sakataren ya?a labaranta, Yusuf Idris Gusau ya sanyawa hannu, ta zargi sabuwar gwamnatin da musanta kar?ar ku?a?en.
Ta kuma mayar wa da sabuwar gwamnatin martani kan zargin tsohon gwamna, Matawalle da sama da fa?i da wasu motocin alfarma wa?anda ta ce an raba su ne ga amfanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.
Tun farko dai gwamnatin jihar ta Zamfara ta bai wa tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa’adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin naira da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ?atan-dabo.
A cewar sanarwar, “idan har sun tashi tabbatarwa, muna sa ran za su ha?a kai da ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin sanin inda motocin suke a maimakon damun Matawalle wanda tuni ya ci gaba da tafiyar da rayuwarsa.
Sanarwar ta kuma bayyana sabon gwamnan a matsayin wanda ba shi da al?ibla.

