Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta tabbatar labarin kisan mutane talatin da hudu da yan bindiga sukayi a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ranar Lahadi.
Mun kawo muku cewa wasu batagari sun kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.
Kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi ranar Litinin, 27 ga Satumba, 2021. A cewarsa, kawo yanzu mutum 34 aka tabbatar da an kashe yayinda Sojoji suka kashe wutar da aka cinnawa gidaje.
“Sojoji sun garzaya wajen kuma suma yan bindigan suka bude musu wuta, amma daga baya suka gudu da suka ji an fi karfinsu.
“Kawo yanzu dai mutum 34 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin. An garzaya da sauran da suka jigata asibiti a jihar Plateau.”
Gwamnan Kaduna ya yi alhinin abinda ya faru, yayi alkawarin biyan kudin jinyan wadanda ke asibiti Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar ya yi Alla-wadai da wannan abu.
“Gwamnan El-Rufa’i ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata dauki nauyin kudin jinyar wanda suka samu raunuka.”

