Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnatin Buhari Ta Fa?i Warwas A Fuskar Tsaro – Jakadan Hayin Banki

An bayyana cewar lalacewar harkar tsaro a karkashin mulkin Shugaban kasa Buhari ya rufe dukkanin wasu ayyuka na cigaba da gwamnatin za ta iya han?oron samu domin rayukan jama’a sune gaba da komai.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba, lokacin da yake tsokaci dangane da kewayowar ranar Dimukura?iyya 12 ga watan Yuni a tattaunawar shi da wakilinmu a Kaduna.

Gambo ya kara da cewa ko shakka babu gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin Buhari ta yi rawar gani wajen gudanar da wasu aikace-aikace da ?o?arin inganta rayuwar al’umma, amma kalubalen tsaro da ya kara lalacewa a mulkin ya zamana ba za’a ga wadancan cigaba ba sai koma baya muraran.

?an siyasar wanda a hannun guda yake rike da Sarautar gargajiya ta Jakadan Hayin Banki Kaduna, ya soki lamirin iyalan marigayi Abiola wadanda ke korafin cewa su ba su amfana da komai ba a sauya ranar dimukura?iyya da akayi daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, inda ya tunatar dasu cewar hikimar sauya ranar domin a tuna da tarihin tsabtataccen za?e da aka yi ne inda ‘yan Najeriya suka yi za?e ba tare da banbancin ?abila ko yanki ba.

Galibin ‘yan Najeriya musamman Arewa suka za?i Abiola suka yi watsi da Bashir Tofa, kuma akayi zaben babu banbancin addini domin Abiola da mataimakin shi Kingibe dukkanin su musulmai ne kuma aka zabe su babu korafi, wannan ne sila sauya ranar dimukura?iyya amma ba wani abu na daban ba.

Daga karshe Abdullahi Gambo Abba ya nemi gwamnatin Buhari da ta ?ara zage damtse wajen shawo kan matsalar tsaro dake addabar kasar fiye da lokutan baya.

Exit mobile version