Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Nasiru Ahmad El Rufa’i ta musanta rahoton da ake ya?awa cewa an samu nasarar cafke ‘yan bindigan da suka sace ?alibai a jami’ar Grienfield dake jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samul Aruwan, shine ya bayyana hakan a wani martani da ya yi kan rahoton kama yan bindigan.
Mr Aruwan yayi maratanin ne a wani gajeren rubutu da yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook ranar Laraba.
Yayin da yake martani kan rahoton, Kwamishina Aruwan Yace:
“Ina ta samun kiraye-kirayen waya, sa?onnin waya, da sa?on email, ana tambaya ta in tambatar da gaskiyar labarin da ake ya?awa cewa an kama yan bindigan da suka sace ?aliban jami’ar Greenfield.”
“Duk da cewa muna bu?atar muga an kama su, amma a halin yanzun ba zan iya tabbatar da sahihancin rahoton dake yawo ba, kuma ni har yanzun ban samu wani bayani daga hukumomin tsaro kan lamarin ba.”

