Site icon Muryar 'Yanci

Goron Sallah: Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya saki fursunoni 123 daga gidajen gyaran hali a fadin jihar a matsayin wani goron sallah a gareshi.

Ganduje, wanda ya sa aka saki fursunonin a gabansa daga gidan Kurkuku na Goron Dutse a ranar Alhamis ya ce anyi musu wannan karamcin ne albarkacin bikin karamar Sallah.

Ya ce an zabi wadanda suka amfana da afuwar ne bisa la’akari da yanayin laifukansu da kuma alamun da ke nuna cewa sun gyaru sun sauya halayensu. Gwamnan ya ce ya yanke shawarar kai ziyara gidan yarin ne domin nuna wa fursunonin cewa gwamnatin jihar ta san da zamansu kuma suma ana daukansu matsayin yan jiha.

Gwamna Ganduje ya ce an saki fursunonin ne bisa tsarin gwamnatin tarayya na kokarin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a kasar. Ya shawarci wadanda aka saki daga gidan gyaran halin su sauya tsarin rayuwarsa sannan su yi wa kasa addu’an zaman lafiya da cigaba.

Tunda farko, Kwantrola Janar na Gidajen Gyaran Hali na Kano, Suleiman Suleiman ya yi wa gwamnan godiya saboda sakin fursunoni da dama tun hawansa mulki. Suleiman ya shawarci fursunonin da aka saki su guji aikata wani laifin da zai saka a dawo da su gidan.

Ganduje ya kuma ziyarci gidajen kananan yara a birnin Kano duk cikin bikin na Sallah.

Exit mobile version