Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sunan Aisha Buhari, na ta kai komo a bakunan ‘yan ?asar musamman a shafukan zumunta tun bayan da ta gayyaci ‘yan takarar shugaban ?asa na dukkan jam’iyyu zuwa shan ruwa.
Babban abin da ya fi jan hankalin shi ne umarnin da ta bayar a katin gayyatar cewa “ba a yarda ku zo da wayoyinku ba”.
‘Yan takara irinsu Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu da Nyesum Wike da Farfesa Yemi Osinbajo da Chris Ngige da Bala Mohammed da David Umahi da Rochas Okorocha aka gayyata da kuma ba su umarta da kada su je da wayoyin nasu.

