‘Yan majalisar wakilai ta tarayya sun yi watsi da kudirinsu, a yanzu ko nan gaba, na yunkurin gayyatar shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, zauren Majalisar don ?arin haske kan matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin arewacin ?asar nan.
A farkon watan da muke ciki ne wasu daga cikin ‘yan majalisa suka gayyaci shugaban ?asa domin jin yadda tsaro ke ?ara ta?arbarewa a yankin arewa biyo bayan yankan rago da kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma 43 a jihar Borno.
Bayanai dake fitowa daga majalisar na nuna cewa, majalisar ta yi watsi da batun kara gayyatar shugaban kasar a yanzu ko nan gaba don yin bayani kan sha’anin tsaro.
Wasu ‘yan majalisar sun bayyana cewa, kiran na da ala?a da siyasa domin cin zarafin shugaban kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
“Mun fahimci cewa ‘yan majalisar ma da suka ?au nauyin kudirin sun bi ta bayan fage sun nemi afuwar fadar shugaban ?asa kan dagewa lallai sai ya amsa gayyatar.”
Tun da fari dai Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai amsa gayyatar majalisar kafin daga bisani ministan shari’a, Abubakar Malami, ya sanar da cewa shugaban kasar ba zai amsa gayyatar ba.
A baya mun kawo muku rahoton cewa wani mamba a majalisar wakilai ta tarayya na gab da shiga tsaka mai wuya sakamakon kiran da ya yiwa majalisar da ta tsige shugaban ?asa bisa gazawa wajen samar da tsaro a Najeriya.
Dan majalisar wakilan, Kingsley Chinda, mai wakiltar Obia/Akpor kuma ?an jam’iyyar PDP, ya bukaci da a tsige shugaba Muhammadu Buhari ranar 7 ga Disamba biyo bayan yankan rago da ‘yan kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma a Zabarmari.
Kazalika, ya ce bai kamata a bar batun kin bayyanar da shugaban kasar ya yi a zauren Majalisar don karin bayani kan ta?arbarewa tsaro ta wuce haka ba salin alin.

