Gwamnatin Najeriya tabi sahun sauran ?asashe wajen yin kira ga Iran da Isra’ila da su yi taka-tsantsan, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa ya?uwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ?asar ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga ?asashen da su duba batun warware rikici cikin lumana, domin samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-?aya.
Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin na a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojinta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai ?aramin ofishin jakadancin ?asar a Siriya, Ranar 1 ga watan Afrilu.

