‘Yan bindiga sun kashe mutum a?alla 26 cikin wasu hare-hare da suka kai a ?auyuka hu?u na Jihar Filato a ranar Lahadi.
Maharan sun far wa ?auyukan ne da ke ?aramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ?ona gidaje masu ?umbin yawa da kuma sace shanu.
Mazauna yankin sun ce an ga gawar mutum 20 a garin Gyambau, sannan an ga wasu shida a Kyaram.
Kazalika, an kai hare-hare a garuruwan Dungur da Kukawa. Mutane da dama ne suka ?ace kuma sakamakon harin.

