Site icon Muryar 'Yanci

Filato: Tsagerun Matasa Sun Hallaka Matafiya ‘Yan Asalin Kano

Labarin dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewa rundunar soji ta Operation Save Haven ta tabbatar da kashe wasu matafiya uku daga jihar Kano tare da jikkata wasu da dama a a hanyar Jos babban birnin Jihar ta Filato.

Mutanen suna kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Nasarawa daga Jihar Kano ne inda wasu matasa a ranar Talata da daddare suka far wa motocinsu a mahadar Bida Bidi cikin karamar hukumar Jos ta Arewa.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa motocin na dauke ne, da fasinja goma ciki har da mace daya.

Majiyarmu ta ce maharan suna dauke da sanduna da adduna lokacin da suka tare motoci.

Wani mutum da ya tsallake rijiya da baya kuma yanzu haka, ke kwance a asibiti, ya bayyana cewa suna tafe sai kawai aka tare motarsu sannan suka afka musu da sara.

Exit mobile version