Kungiyar RDI ta yi tattakin jin halin da alummar yankin Kogin Kolmani suke ciki, tun bayan ayyaka samun ?anyen man fetur da kuma gas a yankin da gwamnatin tarayya ta yi a cikin 2022.
RDI ta nuna ?acin rai ga Gwamnatin Tarayya, ganin cewa har yanzu ba ta fara shirin komai ba dangane da ?aukar matakai da kuma sanar da alummar yankin Kolmani irin illolin da ayyukan ha?ar ?anyen mai kan haifar ga mazauna yankin da ake ha?o man.
?acin rai na RDI ta bijiro ne bayan da ?ungiyar ta yi zaman tattaunawa domin jin ta bakin mazauna yankin a cikin ?aramar Hukumar Al?aleri ta Jihar Bauchi, a ranar 28 ga Fabrairu, 2024.
A wurin jin ta bakin mazauna yankin, sun samu ?arin ilmin sanin matsaloli da Illolin da ka iya shafar su idan aka fara ha?ar ?anyen mai a yankin. An buga masu misalai da irin ibtilaoin gur?acewar muhalli da yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ke fuskanta.
Mazauna yankin na Kolmani sun shaida wa RDI cewa babu wani ?arin haske da suka samu daga Gwamnatin Tarayya.
Sannan kuma yankin na fuskantar rashin jituwa tsakanin mazauna daga jihohin Bauchi da kuma Gombe, inda kowane ?angare ke i?irarin yankin su aka ce an samu ?anyen mai ?in.
Sannan kuma sun yi kuka dangane da yadda ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a yankin, sai kuma yawan gilmawar ba?in da ba a san ko daga ina suke ba, tun bayan ayyana samun ?anyen mai a Kolmani.
Tun a cikin watan Oktoba, 2019 ne dai Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa akwai ?anyen mai har ganga biliyan 1 da kuma kubik biliyan 500 na gas a kwance a ?ar?ashin yankin Kolmani, wanda ya mamaye jihohin Bauchi da Gombe.
An dam?a aikin ha?ar rijiyoyin ?anyen mai ?in ga kamfanin Global Oil, Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas, NNDC da NNPC. Kuma har zuba jarin Dala biliyan 3.
Sai dai kuma babu wani abin da Gwamantin Tarayya ta yi, run bayan raka?i da kwakwazon bayyana an samu ?anyen mai a yankin. Gwamnati ba ta sanar wa mazauna yankin barazanar dagwalon masanaantu mai haifar da illollin gur?acewar muhalli.
Babbar Jamiar Gudanarwar Ayyuka ta RDI, Ifeoluwa Adediran, ta ce: Ko ka?an ba daidai ba ne bayan gwamnatin tarayya ta cika duniya da giringi?ishin samun ?anyen mai, sai kuma ga shi har yau babu wani ho??asa da aka yi domin janyo hankalin mazauna yankin. Sai dai kawai ana yaudarar su ana sanar da su muhimmancin samun ?anyen mai a yankin su.
Ta ce yanzu haka siyasa ta shiga cikin shirin samar da ?anyen mai ?in, inda mutane da dama ke ci gaba da nuna hannu cikin batun alherin da za a samu a yankin.
RDI ta ce za ta ci gaba da wayar wa mutanen yankin kan su domin su san ha??o?in su da yancin su da kuma abin da ka iya taso masu idan aka fara ha?ar ?anyen mai a yankin.

