Mai girma Mataimakin shugaban ?asa, Farfesa Yemi Osinbajo, yace shugaban ?asa Buhari shine ?an siyasar Najeriya da sunan shi ya yi shuhura a wannan zamanin fiye da kowa.
Osinbajo ya fa?i haka ne ya yin ganawarsa da manyan jami’ai a ofishin jakadancin Najeriya na ?asar Birtaniya, a tsakiyar wannan makon da muke ciki.
Mataimakin shugaban yace Sunan da kuma nagartar shugaba Buhari, sune manyan ginshikan da ake bukata wajen kawo ?arshen ?alubalen kasar nan wanda kowa ya gani a yanzu cewa kasar ta dauki saiti.
“Watakila shugaba Buhari shine ?an siyasa a Najeriya da yafi kowanne daukakar suna a wanna zamanin.” “Shine wanda zai je wuri ba tare da ya kira mutane ba, su dakansu zasu zo sauraron jawabin da zai yi. Muna bukatar irin wannan nagartar wajen warware matsalolin ?asar mu.”
“Sabida nagartarsa, duk da abinda ke faruwa a yanzu, shi ka?ai ne zai kirayi kowa, ko da kuwa basa goyon bayansa, amma sun sani cewa shi mutum ne mai fa?a da cikawa.”
“Ko ina kaje a fa?in duniyar nan, mutane na kokarin ha?a kawunan su wuri ?aya, basu son rabuwa, bai kamata mu bari a raba Najeriya ba a yanzun.” “Idan ka duba tattalin arzikin ?ananan ?asashe, zaka ga cewa suna neman hanyoyin ?ara ?arfi ne ta hanyar ha?a kai da wasu.”
Mataimakin shugaban ya yi kira ga yan Najeriya dake ?asashen waje da kuma wa?anda ke zaune a cikin gida, su cigaba da kasancewa a dun?ule, domin kai wa ga mafita.

