Wani kwararren Lauya mai suna Iheanacho Agboti da ke aiki a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, ya yi magana a game da rikicin kungiyar ASUU da jamiar FUTO dangane da batun ba minista Pantami mu?amin Farfesa.
Barista Iheanacho Agboti ya ce a dokar aikin kasa wanda aka yi wa garambawul a shekarar 2005, babu yadda ASUU ta iya da jamiar. Masanin shariar ya ce dokar Trade Union (Amendment) ta 2005 ba ta ba kungiyar ASUU hurumin ta hukunta shugabannin jamia idan su ka saba wata doka ba.
Lauyan ya bayyana wannan ne da yake magana da yan jarida a garin Abakaliki domin yin karin haske a kan abin da doka ta ce a game da surutun da ake ta yi.
Barista Iheanacho Agboti ya caccaki kungiyar malaman jamiar da shiga hurumin da ya fi karfinta. A cewarsa, majalisar da ke sa ido a kan harkar jamia ce kadai dokar Universities Miscellaneous Provisions Act 2012 ta amince ta hukunta shugabannin jamia.
Ni Lauya ne, kuma gaskiya ita ce ASUU ba ta da hurumi a dokar Nigerian Trade Union da za ta dauki mataki a kan shugabannin jamiar FUTO a kan zargin saba doka. Jahiltar gaskiyar lamarin da ASUU ta yi abin takaici ne.

