Aisha Yesufu ta bayyana cewar gwamnatin tarayya ce ta dauko hayar yan daban da suka tayar da hayaniya da kone kone lokacin zanga zangar endsars domin ta lalata shirin da matasan kasar nan ba zanga zangar lumana na kusan kwanaki 8.
‘Yar gwagwarmayar ta bayyana hakan ne a cikin shirin Bakon Mu Na Mako da ake gabatarwa a kafar yanci ta Liberty TV dake birnin tarayya Abuja.
Da aka tambayeta cewar wannan zargi ne babba ko zata bayyana dalilanta na fadin cewar gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin ‘yan daba domin lalata shirin zanga zangar lumana da matasan kasar nan sukayi musamman a babban birnin tarayya abuja da jihar legas.
Aisha Yuseefu ta bayyana cewar tabbas tana da hujjojin da zata iya kare kanta domin akwai faifan video da suke nuna yadda wasu jami’an tsaron kasar nan ke kawo ‘yan daba a motocin alfarma domin su tarwatsa masu zanga zangar lumana, wanda duniya ta gani kuma bayan sun kammala ta’asar su za a zo a dauke su a manyan motoci a maidasu inda aka dauko su.
Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba muhammadu Buhari bata da niyyar kawo karshen matsalolin kasr nan domin bata sauraran mutane kasar domin jin bukatun su shiyasa dole sai an mata zanga Zanga kamin take dawowa cikin hayyacin ta.
Zanga zangar Endsars ya kara bayyano wasu abubuwa da dama a kasar nan, domin in badan sanadin zanga zangar ba, babu yadda za ayi a gano yadda aka boye kayayyakin abincin tallafin korona da aka ba talakawan kasar nan amman azzaluman gwamnonin kasar nan suka boye suka bar mutane cikin yunwa da fatarar.
Yadda ake kashe mutane a yankin arewacin kasar nan babu wani anfani da shugaba Buhari ya yi wa arewa duk da kasancewar sa dan arewa tare da goyon bayan da yasamu daga yankin.
Yanzu ta kai matsayin da a arewacin kasar mu sai manoma sun biya yan ta’adda haraji kamin su iya kwaso kayayyakin da suka noma kuma saboda son zuciya irin na mutanen mu na arewa ace ankasa fitowa a kalubalanci shugaba Buhari ta hanyar zanga zanga saboda kawai shi dan arewa ne.

