Site icon Muryar 'Yanci

#EndSARS: ?ungiyoyin Musulmi Dana Kirista Sun Yi Martani Ga Fadar Shugaban Kasa

?ungiyar Kiristoci a Najeriya da Kwamitin ?oli na harkokin addinin musulunci sun soki lamirin fadar shugaban ?asa kan dora musu laifin haifar da zanga zangar EndSARS da zargin su da rura wutar fitinar.

Hadimin shugaban kasa Femi Adesina cikin wani rubutu da ya wallafa a ?arshen makon da ya gabata, ya ce sakonnin ?iyayya da ke fitowa daga Masallatai da Coci-Coci suna da ala?a da zanga zangar #EndSARS wadda ta ?i ci ta ?i cinyewa.

?ungiyoyin Musulmi dana Kiristocin a mabanbantan hira da suka yi, sun soki fadar shugaban kasar kan abinda suka kira dora laifi kan wasu a maimakon magance matsalar da ta taso.

A rubutun da Adesina ya wallafa mai taken, ‘Idan Najeriya ta mutu, ?iyayya ce ta kashe ta,’ ya ce zanga zangar EndSARS dama ce ta ya?a sakonnin ?iyayya da masallatai da coci ke da hannu ciki.

A martanin da CAN ta bayar ta bakin Fasto Bayo Oladeji, ya bayyana cewar:
“Yana da wahala a gano ko Femi Adesina yana fadin son ransa ne ko abinda ke zuciyar mai gidansa”. Matsalar wasu hadiman gwamnati na samo asali ne da zarar sun fara tunanin sun fi kowa son Najeriya.
Wannan abin takaici ne kuma ba daidai bane.”

A bangaren ta, Kakakin NSCIA, Ustas Ibrahim Aselemi, ya ce, “NSCIA ta yi aiki sosai don wayar da kan shugabannin masallatai a Najeriya game da sharrin da ke tattare da kalaman ?iyayya.
“A lokuta da dama, Majalisar ta kan nemi gwamnatin tarayya ta hukunta wasu da ke ya?a kalaman ?iyayya.

Majalisar ta gargadi limamai da dama cewa wannan ba shine ?ancin fa?in ra’ayi ba. Don haka ban san inda Kakakin Shugaban ?asa ya samo wannan bayanin ba.”

Exit mobile version