Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tsinewa ?an bindiga da masu ?aukar nauyin su a ?asar nan.
Wa?annan na daga cikin kalaman gwamna El-Rufai a lokacin da yake jawabi ga ?an jihar a tattaunawa da yayi da tashoshin radiyo na jihar a fadar gwamnatin jihar ranar Talata.
El-Rufai ya ce za a toshe layukan sadarwar wasu kananan hukumomi da ?an bindiga suka tsananta kai hare-hare da zarar jamian tsaro sun bu?aci a yi haka.
Bayan kammala wannan tattaunawa da yayi da jawabi ga ?an jihar ranar Talata, kwamishinan tsaron jihar ya yi ganawa da ?an jarida ranar Laraba inda ya bayyana sabbin matakan da gwamnati ta ?auka bayan toshe hanyoyin sadarwar jihar.
Ga tattaunawar
Gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da kabukabun acaba daga ranar Laraba, 29 ga Satumba, ba za su sake fita aiki ba sai kuma wada Allah yayi.
Hakan da wasu dokoki na kunshe ne a doguwar jawabi da kwamishinan tsaron jihar Kaf na yayi ranar Laraba a Kaduna.
A cikin jawabin Samuel Aruwan ya ambato wasu matakai da gwamnati ta dauka bayan hana ?annacaban da aka yai kamar haka:
Duk wanda aka kama dauke kowani irin makami zai ?an?ana ku?ar sa.
?an Keke-Napep za su rika aiki ne daga karfe 7 na safe zuwa shida na yamma, idan ka kuskure su kuma sai ka tako zuwa gida.
Duka motocin haya da zasu rika aiki a Kaduna dole su yi fentin ruwan kwai da baki, haka kuma wa?anda ke aikin tasi-tasi.
Babu siyar da mai a jarkoki a kananan hukumomin Birnin Gwari, Kauru, Kachia, Kajuru, Chikun Giwa, Igabi, Kagarko.
An hana safarar itace da gawayin girki a motoci, shiga ce ko fita.
An dakatar da cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da babbar kasuwar mako-mako da ake ci duk Talata ta Kawo.
Gwamnati ta ce an ?auki wannan makati ne domin a jamaa ba don son rai ba.
Wasu mutane ?alilan sun jefa mutane da yawa cikin halin ?a?anikayi babu gaira babu dalili. Ba za a bari hakan ya ci gaba ba, dole a bi duk hanyar da za abi a kawo harshen wannan masifa a ?asar nan.

