Site icon Muryar 'Yanci

El Rufa’i Na Cikin Wa?anda Suka Iza Buhari Suka Gaza Fidda Shi – Ortom

Gwamnan Bunuwai, Emmanuel Ortom ya maida wa gwamnan jigar Kaduna Nasir El-Rufai martani zargin wai ya zargi gwamnan da yin amfani da rashin tsaro a jihar sa da ya kasa warwarewa sai dangana shi yake da wai gazawa ce daga bangaren gwamnatin tarayya.

Ortom ya ta hannun Kakakin sa ya shaida cewa wannan magana da suka karanta bai yi musu dadi ba domin bai kamata ace kamar El-Rufai bane dake da guntun kashi a bayan sa zai fita yana irin wannan magana.

” Na fi karfin El-Rufai ya yi min Izgilanci domin shine abin tausayi, wanda matsalolin da ya kirkiro da hannun sa suka dabaibayeshi ya kasa warware su, ya kyale mutanen kaduna na ta iyo cikin kogin wahala da rashin zaman lafiya.

” El-Rufai mai ci da addini ne, domin kowa ya san yadda ya ?auki gatari ya datsi zaman soyayya dake tsakanin ‘Yan Kaduna aka samu rarrabuwa a jihar,kuma ya kasa magance matsalolin.

” Kai bari in gaya muku karara ku saurareni, El-Rufai na daga ciki, wadanda suka kai Buhari suka baro a kasar nan. Ba shi da hurumin da wai ace yau El-Rufai ne zai zargi gwamna Ortom na rashin tabuka komai.

” Kwana-kwanan nan ya kori ma’aikata akalla dubu 4000 a jihar sa. Wannan mutum ne mai tausayi. Bashi da ita.”

A takardar martanin da Ortom ya fitar wanda Channels TV ta wallafa a shafin ta na yanar gizo ta inda Ortom ke shiga bata nan yake fita ba.

Ortom ya ce ruwa ne yake neman ya kare wa El-Rufai, Buhari ya fara nesa-nesa da shi, s hine ya ke so ya burge fadar shugaban kasa ta hanyan haurar gwamna Ortom.

Exit mobile version