Site icon Muryar 'Yanci

El Rufa’i Mutum Ne Mai Kunnen ?ashi – Dr Ar?o

An bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El Rufa’i a matsayin wani mutum hutsu mai kunnen ?ashi wanda bai damu da halin da jama’ar Jihar shi suke ciki ba gaba ?aya.

Wani mai fashin ba?i akan harkokin siyasar Najeriya Dr Umar Ar?o ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai da ya yi a kaduna a wajen taron karrama ?aliban kwalejin koyon dabarun noma dake Afaka wa?anda aka ceto daga hannun ‘yan bindiga ?arkashin jagorancin Sheikh Dr Ahmad Gumi.

Dr Ar?o ya ?ara da cewar taurin kai da kunnen ?ashi na Gwamna El Rufa’i shine silar jefa rayuwar jama’a musamman daliban manyan makarantu cikin hatsari na fargabar mamayar ‘yan Bindiga.

“Ya kamata El Rufa’i ya sani cewa wadannan dalibai da ‘yan bindiga suka sace ‘ya’ya ne na jihar Kaduna, suna da hakki a kashe ko nawa ne wajen ceto su daga hannun ‘yan bindiga, domin tabbas rai ya fi dukiya”.

Dr Ar?o ya yaba namijin kokarin da sanannen malami Dr Gumi ya yi na shiga gaba wajen ceto ?aliban, sannan ya tabbatar da cewa shirye shirye sun yi nisa wajen ceto ?aliban jami’ar Greenfield dake hannun ‘yan bindiga wa?anda El Rufa’i ya yi watsi da sha’anin su.

Dr Ar?o ya tabbatar da cewa sulhu da ‘yan bindiga shine mafita, kuma muddin aka bi wannan tafarki babu shakka za’a kai ga nasara.

Exit mobile version