Site icon Muryar 'Yanci

EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Nasarawa Da Matarshi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa bisa ga zargin cin amanar kasa.

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa cewa a halin yanzu jami’an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.

Al-Makura ya rike mukamin gwamnan Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 kafin aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a jihar.

Da aka tuntube shi game da batun, kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce kawo yanzu ba a masa bayani a kan lamarin ba.

Tsohon mai magana da yawun gwamnan, Danjuma Joseph, ya ce bai da masaniya a kan lamarin a yayin da ake tuntube shi. Joseph ya ce: “Mai girma ya bar Lafia (babban birnin jihar Nasarawa) a safiyar jiya don zuwa Abuja.

Bani da labarin an kama shi.” Hukumar ta EFCC bata taba bincikan tsohon gwamnan ba a baya. Hasali ma, hukumar ta EFCC ta taba taimakawa gwamnan da iyalansa a lokacin da wani dan damfara ya ya yi kokarin damfarar gwamnan a 2018.

Exit mobile version