Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce jamianta sun yi nasarar cafke wasu matasa su 10 da ake zarginsu da damfara mai nasaba da kwamfuta da ake kira Yahoo-Yahoo.
Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ta EFCC, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a makarantarsu ta Academy da ke yankin Bwari na birnin Abuja inda aka ce su su na koyon sanaar yaudarar mutane ne.
Wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 30, su ne Sixtus Jude, Moses Samuel, Isalan Johnny, Dapet Nimshak, Samuel Ogboche, Victor Samuel, Victor Asuquo, Ibrahim Yunusa, Yahaya Usman da Chijoke Ikwuoha.
Harkar damfara a kafafen sada zumunta na zamani na nema zaman ruwan dare a tsakanin Matasa a Najeriya, wanda hakan ya sanya a kusan kullum ake samun tarin matsaloli na damfarar jama’a a fa?in ?asar.

