Site icon Muryar 'Yanci

ECOWAS Za Ta Kafa Dakaru Na Musamman Domin Yakar Ta’addanci A Yammacin Afirka

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu i?irarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ?asashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Najeriya ya rawaito.

Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne jiya a Abuja cewa ?ungiyar na bukatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ?asashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin.

“A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin kasa mafi fama da ta’addanci a duniya kuma Afirka ta zama gida ga kungiyoyin ta’addanci,” in ji Musah.

Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga kungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin al-Qaeda da IS a tsawon shekaru.

Exit mobile version