Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya ya bayyana cewa karmata ‘yan wagga fargaba idan ?an ?abilar Igbo ya zama shugaban ?asa, yana mai cewa jiharsa “ba za ta ta?a shiga yun?urin kafa ?asar Biafra ba”.
Kazalika gwamnan ya ro?i hukumomin Najeriya da su mur?ushe duk wanda ke son tayar da hankali a yankinsu na kudu maso gabas.
Umahi wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya fa?i hakan ne a Abakaliki babban birnin jihar ranar Alhamis yayin wata liyafa da aka ha?a masa.

