Site icon Muryar 'Yanci

Duk Shugaban Da Ya Yi Rantsuwa Da Littafin Allah Ya Ji Tsoron Cin Amana – Buhari

Rahotanni daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa kwanakinsa a matsayin shugaban kasar Najeriya kayyadaddu ne kuma komai jimawa ko dadewa zai zama tsohon shugaban kasa.

A saboda hakan ne shugaban kasan ya shawarci shugabanni da suka yi rantsuwa da littafan addini ya zama dole kada su ci zarafin wannan yardar da aka basu ta shugabanci.

Buhari yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Nasarawa ya jaddada cewa bashi da niyyar cigaba da zama a mulki fiye da tanadin kundin tsarin mulki. Kamar yadda yace, “Sarautar gargajiya ita har karshen rayuwa ce. Amma a kundun tsarin mulki, mu ba hakan bane. Ba zan iya wuce wa’adin mulki biyu ba kuma na dauka rantsuwa da Qur’ani cewa zan kiyaye kundin tsarin mulkin Najeriya.

Dole ne mu tabbatar da cewa ba za mu iya cin amanar da Allah ya bamu ba a matsayinmu na shugabanni. “Ban taba ganin tsohon gwamna a nan ba, nima tafiya zan yi wata rana,” yace.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga jama’ar jihar Nasarawa kan tarbar da suka yi masa inda ya bayyana farin cikinsa kan kyan da ya ga jihar ta yi tun bayan ziyarar da ya kai 2019.

Exit mobile version