Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin ?aukar tsattsauran mataki kan Yan ta’addan Daji Matukar Suka Shigo Masa jiha..
Gwamna Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya kar?i bakuncin shugaban ?aramar hukumar Yagba West, Pius Kolawole, domin tattaunawa kan fashi da makami a yankinsa da kuma matakan da aka ?auka.
Gwamnan Ya ?ara jaddada kudirin gwamnatinsa na ha?a kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta’addanci ba tare da tausayi ba.

