Site icon Muryar 'Yanci

Dole Musulmi Su Kafa Ta Su Majalisar Dinkin Duniya – Erdogan

Shugaban ?asar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya bayyana cewa tunda majalissar ?inkin duniya, ba za ta iya share hawayen ?asashen Musulmin duniya ba to bata da amfani suci gaba da zama a cikinta, duba da yadda ake ta hallaka musulmin ?asar Palas?inawa, wanda Isra’ila ke yi amma ba tare da majalissar ?inkin duniya ta ?auki wani mataki na hana faruwar hakan ba.

Erdogan ya ce, “ya zama wajibi mu kafa sabuwar majalissar ?inkin duniya ta Musulunci (Muslim United Nations) domin kuwa abubuwan da ake yi na kisan musulmi tare da aibata su da sunan ?an ta’adda hakan ba abun da zamu kyale bane, in ji shi, a wani jawabi da yayi a daren jiya a kafar talabijin ?in kasar.

Muna fatan Allah ya taimaki wannan bawa na sa dake son kare addinin Musulunci da Musulmi, amin.

Exit mobile version