Site icon Muryar 'Yanci

Dan Bindiga Bello Turji Ya Karyata Labarin Kama Baleri

IMG 20240312 WA0021

Gawurtaccen ?an bindigar nan na Najeriya Bello Turji ya ?aryata i?irarin da sojojin Nijar suka yi na kama mashahurin ?an bindigar nan Baleri Fakai.

Cikin wani bidiyo da ya kara?e shafukan sada zumunta, an ga Bello Turji, kewaye da maya?ansa ri?e da muggan makamai, ya nuna wani mutum da ya ce shi ne Balerin, ba wanda sojojin Nijar suka ce sun kama ba.

Dama dai a makon da ya gabata ne Jaridar PRNigeria ta yi wani bincike da ta tabbatar da cewa mutumin da sojojin Nijar suka kama sunansa Kachalla Baleri, ba Baleri Fakai da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo ba.
Turji ya ce ”sun ce sun kama tare da kashe Baleri, to amma fa ga Baleri”.

Cikin bidiyon mai tsawon minti ?aya da sakan 29, Bello Turji ya zargi gwamnatocin Nijar da Najeriya da kamawa tare da kashe mutanen da ba su ji, ba su gani ba a matsayin ‘yan bindiga.

Sojojin Najeriya sun bayyana samun gagarumar nasara dangane da kamen da sojojin na Nijar ?in suka yi, to sai dai binciken PRNigeria da wannan sabon bidiyon ka iya aza ayar tambaya kan sahihancin i?irarin nasu.

Exit mobile version