Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ?asar, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
?an takarar shugaban ?asa a za?en 2023 a ?ar?ashin jam’iyyar PDP ya kai ziyarar ne tare da rakiyar wasu manyan abokan siyasarsa.
A sa?on da Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ?asar ya ce ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne domin yin ”gaisuwar Sallah”
Ziyarar ta Atiku Abubakar ta zo ne kwana uku bayan ya ziyarci tsaffin shugabannin Najeriya, Ibrahim Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar a gidajen su da ke jihar Niger.
Ana dai ala?anta irin wannan ziyara da shirye shiryen babban za?en 2027.

