Mataimakin Gwamnan Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya bayyana wa BBC matsayinsa, inda ya ce yana nan daram a jamiyyarsa ta PDP bayan gwamna Bello Matawalle ya sauya she?a zuwa Jamiyyar APC a ranar Talata.
“Tun asali a nan nake tun mahaifi na ya kawo jamiyyar ba mu taba barin PDP ba, nan aka same mu kuma nan za mu tabbata, in ji shi.
Mahdi Aliyu Gusau ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin jamiyyarsa ta PDP na garzayawa kotu domin ?watar kujerarta ta gwamna da kotun ?oli ta najeriya ta ba ta, tare fatan mulki zai dawo hannunsa.
Duk da mataimakin gwamnan na Zamfara ya ce babu wata matsala tsakaninsa da gwamna Bello Matawalle amma ya ce gwamnan bai nemi shawararsa ba har zuwa lokacin da ya yi wanka zuwa jamiyyar APC.

