Tsohon Jarumin finafinai hausa na Kannywood Sani Mai Iska kuma tsohon mijin fitacciyar jarumar nan wadda a shekarun baya tayi suna Fati Muhammad ya bayyana labarin yadda rabuwar auren su ta kasance da jarumar.
Mai Iska ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi dashi cikin shirin “Daga Bakin Mai Ita’.
Jarumin ya bayyana cewa rabuwar tasu ta faru ne da sanin kowa domin babu wanda yake da laifi a cikin su, kawai dai tabi umarnin Mahaifiyar ta ne.
Sannan ya kara da cewa yayi mata saki biyu ne kacal, Amma kuma ita ta bayyana cewa saki uku ne wanda ba haka maganar take ba.

