Site icon Muryar 'Yanci

Dalilin Da Ya Sa Muke Cin Bashin Da Ya Fi Karfinmu – Fadar Shugaban Kasa

Ministar harkokin ku?a?e Zainab Ahmed ta bayyana cewa babu wata mafita sai Najeriya ta ciwo bashi sannan ta ke iya yin ayyukan raya ?asa.

Zainab na fito ?arara ta bayyana wannan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki ne, yayin da ta ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta ?asa mai Lura da harkokin ku?a?e, a ranar Laraba.

Ta bayyana gaban kwamitin tare da Daraktan Ofishin Lura da Basussuka, wato DMO, Ben Akabueze, Akanta Janar na Tarayya na ri?o, Okolieboh Sylva da wasu jami’ai.

Ta ce zuwa watan Agustan da ya gabata bashin da aka ciwo ya kai naira tiriliyan 5.33, saboda haka ya zarce ?a’idar gejin adadin da ya kamata a ciwo bashi da naira biliyan 430.82.

Ta ce a cikin Yuli kuwa bashin ya zarce geji da naira tiriliyan 1.26.

Najeriya ta sake yin sabon shirin ciwo bashin naira tiriliyan 8.2 domin wasu daga ayyukan da ke ?unshe cikin kasafin 2023.

Idan za a tuna kuma, ?an takarar shugaban ?asa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya bayyana cewa bashin da gwamnatin Buhari ta ciwo ba shi da illa, duk cikin aiki ne.

Tinubu ya ce tulin bashin da Buhari ya ciwo ba illa ba ce, duk cikin aikin ne.

?an takarar shugaban ?asa a ya bayyana cewa masu aibata Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa saboda sun ciwo bashi, ba su yin zurfin tunani.

Tinubu ya ce yawan bashin da Gwamantin Buhari ta ciwo ko ya ke kan ciwowa, ba illa ba ce, domin ayyukan raya ?asa ake yi da ku?a?en.

Ya yi wannan furucin a lokacin da Buhari ke ?addamar da Kwamitin Kamfen ?in TInubu da Shettima a Abuja.

A wurin ?addamarwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa rayukan ‘yan Najeriya za su fi garantin samun kyakkyawar kulawa a hannun APC fiye da sauran jam’iyyu masu takarar shugaban ?asa a za?en 2023.

Buhari ya ce ya zama wajibi a yi duk irin ?o?arin da ya dace domin a ga APC ta ci gaba da mulki, yadda ‘yan Najeriya za su ci gaba da cin alherin da APC ta kawo a ?asar nan.

Yayin da ya ke jinjina wa ?an takarar shugaban ?asa na APC, Bola Tinubu, Buhari ya kuma jinjina wa dukkan sauran ‘yan takarar da su ka yi za?en fidda gwani tare da Tinubu, amma su ka janye masa, ko kuma ya kayar da su.

Ya ce babu wata jam’iyyar da ta dace da ‘yan Najeriya sai APC.

Da ya ke jawabi, Tinubu ya jinjina wa Buhari da kuma gwamnatin sa, tare da cewa idan ya hau mulki, zai ?ora daga inda Gwamnatin Buhari ta tsaya.

An dai ?addamar da Daftarin ?udirorin APC, wato APC manifesto, mai shafuka 80, wanda cike ya ke da wasu al?awurran da APC ta ?auka tun a 2015, amma har yau ba ta cika ba.

Shugaban Kamfen ?in TInubu 2023, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce ya zama wajibi duk wani ?an kwamitin kamfen ya tashi tsaye wurjanjan ya yi aiki tu?uru.

Exit mobile version