Shugaban hukumar kula da ababan hawa da muhalli ta jihar Kaduna, KASTELEA wato Manjo Garba Yahaya Rimi, kuma shugaban kwamitin ya?i da annobar korona a jihar ya bayyana wa BBC cewa kai samamen na daga cikin matakan da suka fara ?auka na da?ile annobar korona.
A ranar Laraba ne gamayyar jami’an tsaro suka kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan matakin ba wai ya tsaya bane kan makarantar Dahiru Bauchi ka?ai, inda ya ce ya shafi duka ?ananan hukumomi 23 ne na jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ?alibai 140 suka kwasa daga makarantar kuma an ajiye su sansanin alhazai na jihar Kaduna inda ake tantance su, inda ya ce akwai wasu daga cikin almajiran da suka fito daga ?asashe kamar Nijar da Chadi.
Gwamnatin ta ce idan aka gama tantance almajiran, wa?anda suka fito daga wasu jihohi za a mi?a su ga gwamnonin jihohinsu, na jihar Kaduna kuma za a mi?a su ga ciyamomi na ?anan hukumomi, ?aliban ?asar waje kuma za a mi?a su ga hukumar shige da fice ta Najeriya.
Ko a bara sai da gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da ya?a korona.

