Rahotanni daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya na bayyana cewar ?asar Saudi Arabiya ta maida martani kan mutanen dake sukar matakin da ta ?auka na rage ?arar kiran sallah a masallatai.
Idan masu karatu za su tuna mun kawo muku rahoton cewa Saudiyya ta bada umarni ga masallatai su rage ?arar lasifikokin su yayin kiran sallah.
Rahoton BBC ya nuna cewa ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta ?asar ta maida martani kan wasu mutane dake sukar matakin.
Abdul-lateef Sheikh ya bayyana cewa an ?auki wannan matakin ne biyo bayan ?orafe-?orafen da jama’a ke yi kan ?arar kiran sallah.
Daga cikin wa?anda suka yi ?orafin kan ?arar ?iran sallah, akwai iyaye wa?anda suka bayar da dalilin su cewa ?arar lasifikun masallatai na hana ‘ya’yansu barci.
A makon da ya gabata ne, ma’aikatar ta umarci masallatai a ?asar su rage ?arar na’urar kiran sallah zuwa kashi ?aya na ?ararta.
“Masu sukar wannan matakin ma?iya ne kuma masu son tada husuma a tsakanin jama’a.” Inji shi.

