Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya je karutun digiri na biyu ne a ?asar waje, shi ya sa ba ganin sa a tarukan jamiyyar PDP.
Atiku ya bayyana haka a wajen taron kwamitin amintattun jamiyyar da ake yi a halin yanzu.
Ya ce ya yi digiri na biyu ne a kan harkokin kasa da kasa, kuma ya kammala karatun nasa, saboda haka a nan gaba ba zai na yawaita bulaguro ba.
An dade ba aji duriyar Atiku a cikin PDP ba tun bayan da rikicin cikin gida ya barke a cikin jam’iyyar wanda ya yi sanadin sauke Shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondos.

