Site icon Muryar 'Yanci

Dalilan Da Ya Sa Bano Goyon Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya mayar da martani kan wani tsohon bidiyo da ake ta ya?awa a shafukan sada zumunta wanda ke nuna shi yana sukar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kan ?in biyan ku?in fansa don ku?utar da ?an matan Chibok.

Gwamnan ya ce an na?i bidiyon ne a shekarar 2014 bayan sace ?aliban makarantar ta Chibok, wanda kuma ya ke zargin Jonathan da rashin sanin aikinsa sannan ya bu?aci ya bi duka hanyoyi wajen ganin an ku?utar da ?an matan ko da kuwa tattaunawa ce da maya?an Boko Haram.

Sai dai wata sanarwa da aka fitar mai ?auke da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai bai wa gwamna El-Rufa’i shawara kan sadarwa, ta ce tun daga shekarar 2014 kawo yanzu, salon da ?an bindiga suka ?auka ya sauya.

Kuma shi ya sa a yanzu El-Rufa’i ba ya goyon bayan biyan ku?in fansa ko tattaunawa da ?an bindiga.

Sanarwar ta ce masu yada bidiyon ba su yi la’akari da halin tashin hankalin da gwamnan da al’ummar jihar Kaduna suke ciki ba, amma suke sukar El-Rufa’i don ya jaddada manufarsa ta son bin doka da ?a’ida na ?in son biyan ku?in fansa da yin sulhu da ?an bindiga.

Haka kuma, sanarwar ta ce idan aka yi la’akari da jerin sace-sacen mutane da ?alibai da suka auku a Najeriya a shekarun nan, ana iya fahimtar cewa biyan ku?in fansa da yin sulhu ba su ne za su kawo ?arshen matsalar ba, illa ma dai su ?ara wa maharan ?arfi.

Sanarwar ta ce duk da cewa matsalar tsaro ta yi wa Najeriya dabaibayi, bai kamata a biye wa ?an bindigar ba wajen ba su ku?in fansa wanda suke samu su sai makamai.

A watan Maris ne ?an bindiga suka sace ?alibai daga wata makarantar gaba da sakandire a unguwar Mando a jihar ta Kaduna kuma suka bu?aci a biya ku?in fansa don sako ?aliban amma kawo yanzu gwamnatin jihar ba ta biya ku?in ba don haka suna hannun ?an bindigar.

Haka kuma, a farkon wannan watan na Afrilu ma an sace wasu ?alibai daga jami’ar Greenfield duk a jihar ta Kaduna kuma kawo yanzu masu garkuwan sun kashe biyar daga cikin ?aliban.

Gwamna Nasir El-Rufa’i dai ya da?e yana bayyana cewa bai amince da sulhu da biyan ku?in fansa ba ga ?an bindiga. Ya ce kamata ya yi a kawo ?arshensu da ?arfin tsiya ta hanyar yin fito na fito da jami’an tsaro.

Exit mobile version