Babban Bankin Najeriya CBN yace ko ka?an ba zai cire haruffan larabci da ke jikin Naira ba, domin wadannan harrufa na Ajami ba suna magana ba ne akan cewar ku?in na Musulunci ne.
Bankin ya bayyana wannan matsayi ne a yayin mayar da martani dangane da korafin da wasu ke yi na cewar a gaggauta cire harrufan larabci jikin Naira kasancewar Najeriya ba ?asar Larabawa ba ce.
A kwanakin baya ne wani babban Lauya mazaunin Legas mai suna Barista Malcolm Omirhobo ya shigar da ?ara gaban Babbar Kotun Jihar Legas yana bukatar a gaggauta cire harrufan larabci a jikin ku?in Najeriya.
A cewar Lauyan barin wa?annan harrufan to kamar yana nuni da cewar Najeriya ?asar Musulmi ce wanda ko ka?an abin ba haka ba ne inji shi.
Sai dai tuni Lauyan Babban Bankin Abiola Lawal ya wanke wannan tunani na Lauya Malcom, inda yace rubutun ajami a jikin ku?in Najeriya bai nuna cewar Najeriya ?asa ce ta musulunci, sai dai kawai an samar da wannan tsarin ne, domin ya taimakawa ‘yan kasuwa wa?anda ba za su iya karanta turanci ba, saurin fahimtar rubutun na larabci wanda suka saba da shi.
Ya ?ara da cewar rubutun ajami a jikin ku?in Najeriya ya samo asali ne tun lokacin Turawan mulki, kuma basu bayyana larabci a matsayin harshen ?asa ba.
Hakazalika bu?atar Lauya Malcom ta kara gamuwa da cikas a karar da ya shigar akan rundunar sojojin Najeriya yana bukatar a cire kalmar Larabci a jikin Logon kayan Soji.

