Site icon Muryar 'Yanci

Dalibai Za Su Fara Cin Gajiyar Bashin Karatu A Makon Gobe

images 2024 03 14T070645.613

?aliban manyan makarantun gwamnatin tarayya a Najeriya da suka nemi bashin ku?in karatu za su fara samun ku?in nan da mako ?aya, a cewar asusun ba da bashin ?aliban.

Sai dai shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce ?aliban makarantun da za su fara sabon zangon karatu ne kawai za su ga ku?in a asusunsu a yanzu.

A jiya Laraba ne Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ?addamar da asusun mai suna Nigerian Education Loan Fund (Nelfund) a hukumance a fadar shugaban ?asa da ke Abuja.

Mista Sawyerr ya ce jimillar ?alibai 170,000 ne suka yi rajista da asusun, wa?anda suka ?unshi ?aliban jami’a, da na kwalejojin ilimi da fasaha.

“A ta?aice dai, jimillar ?alibai 110,000 ne suka nemi bashin. Sun ba da bayanansu tare da mi?a takardun neman, kuma su ne suka cancanta. Amma duk da haka za mu ?ara gudanar da bincike a kansu… Amma da alama sama da mutum 110,000 ne za su fara samun bashin a sati mai zuwa,” in ji shi.

Exit mobile version